Dambun shinkafa da zogale

Fatima Ahmad(Mmn Adam) @cook_16332540
Dambun shinkafa da zogale
Umarnin dafa abinci
- 1
Idan an barzo shinkafa sai ki wanke ki tace ki zuba a matsamin da zakiyi dambu dashi(madambaci)
- 2
Sai ki samu tukunya wadda zaki dora madambaci akai yadda iska bazai fito ba, ki zuba a tukunyan ki dora madambaci akai sai ki dora a wuta ki rufe yadda iska bazai shiga ba.
- 3
Idan ya turara na 10mins sai ki juye a wani kwano ki sa jajjage attaruhu da albasa, mai, kayan kamshi da sinadarin dandano, da gyada da zogale da kika gyara. Ki garwaya ko ina ya samu hadi.
- 4
Sai ki mayar cikin madambacin ki sake turarawa ba minti 10 shikenan ki sauke.
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/10515521



sharhai