Peteto Roll

TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA)
TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA) @cook_15480513
Port Harcourt

Yanada dadi sosai kuma yanada saukin yi zaki iyayiwa yara don zuwa makaranta #SSMK

Peteto Roll

Yanada dadi sosai kuma yanada saukin yi zaki iyayiwa yara don zuwa makaranta #SSMK

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Fulawa kofi biyar
  2. Butter rabin kofi
  3. chokaliGishiri rabin
  4. Ruwa kofi daya da quarter
  5. Kayan hadi na ciki
  6. Dafaffen dankalin turawa guda biyar
  7. Albasa
  8. Kayan dandano
  9. Curry
  10. Alaiho dan kadan
  11. Corn flour chokali biyu
  12. Thyme
  13. Sai mai don soyawa

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Ga kayan hadina nan

  2. 2

    Zakitankade fulawarki kizuba a bowl sai kisa butter da gishiri kijujjuya sai kizuba ruwa kikwabashi sannan ki rufe ki ajiyeshi na minti biyar zuwa shida

  3. 3

    Sai kifere dankalinki kixuba a tukunya kisa ruwa da gishiri dan kadan kibarta tanuna luguf sai kisauke kizuba a turmi ki dakata da kyau sai kijuye kisa albasa attarugu alaiho da maggi tareda curry da thyme da corn flour sai kijujjuya komai yahade wuri daya sai kishafa mai ahannunki kina mulmulasu kanana kina ajiyewa a gefe har kigama

  4. 4

    Sai kidauko kwabin fulawan kisake kwabawa sai kirabashi kashi uku sai kibarbada fulawa a wurinda zaki murzan sannan kidau daya kimurzata da fadi sannan da tsayi sai kidau uka kirabata kashi uku ko hudu sai kidau dankalinda kika mulmulan kidaura akan ko wanne sannan kinannade shi idan yakai rabi sai kiyanka kidanne bakin da toothpic sai ki ajiye agefe.

  5. 5

    Haka zakirikayi har kigama sai kidaura mai awuta idan yayi zafi sai kidan rage wutan sannan kifara soyawa. Shikenan kingama zaki iya cinsa da ketchup ko chocolate source kokuma miya

  6. 6

    Shikenan acidadi lfy

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA)
rannar
Port Harcourt
Gskiya arayuwata inason girki sosai shiyasa kullum ina kicin wurin tsara abinci kalakala
Kara karantawa

Similar Recipes