Kunun gyada

Masu dafa abinci 3 suna shirin yin wannan
Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

minti talatin
hudu
  1. Nikakkiyar gyada-kopi daya
  2. Cous cous manya-kwatan kopi
  3. Kimba-kadan
  4. Bushesshiyar citta-kadan
  5. Siga-dai dai yanda kike bukata
  6. Fulawa-kwatan kopi
  7. Tsamiya-rabin kopi

Umarnin dafa abinci

minti talatin
  1. 1

    Dafarko xaki dama nikakkiyar gyadanki da ruwa ya damu sosai sai ki taceshi acikin tukunya da rariya kidaura akan wuta

  2. 2

    Sai kiwane kimba kisa

  3. 3

    Kiwanke bushasshen citta kisa sai ki rufe ki barshi ya tafaso amma karki matsa daga wajen gudun xubewa kibarshi yayita tafasa harsai yadai na tafasowa shine zakigane gyadar ta nuna

  4. 4

    Sai kisaka cous cous din kunu ki gauraya kibarshi har ya nuna

  5. 5

    Idan cous cous din yanuna sai kidama fulawa da ruwa

  6. 6

    Sai kijuye akan kunun kina gaurayawa har sai kaurin yamiki yanda kikeso,ba aso kiyishi da kauri sosai saboda idan yahuce kara kaurin xeyi

  7. 7

    Sai ki xuba siga ki gauraya kibarshi yadan tafaso kaman minti biyu haka sai ki sauke.

  8. 8

    Asha dadi Lpia.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Najma
Najma @cook_12709285
rannar
Kano State
cooking is my portion
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes