Farfesun kayan ciki mai dankalin turawa da kayan lambu

Hauwa Bunza
Hauwa Bunza @Hauwabz09
Sokoto

#Sokotobake
Yana cika ciki ko shi kadai kasha

Farfesun kayan ciki mai dankalin turawa da kayan lambu

#Sokotobake
Yana cika ciki ko shi kadai kasha

Edit recipe
See report
Share
Share

Ingredients

  1. Kayan ciki
  2. Tattasai,tarugu da albasa
  3. Dankalin turawa
  4. Karas
  5. Pea
  6. tafarnuwaQarin citta da
  7. Kayan dandano
  8. Kori
  9. Mai kadan

Cooking Instructions

  1. 1

    Za'a yanka kayan ciki a wanke sosai kar a saka hanji

  2. 2

    Sai ki zuba a tukunya ki dora a wuta kisa ruwa isashe, albasa, da dan gishiri kadan,ina kina cin farin mafi a saka da garin citta da tafarnuwa

  3. 3

    Sai ki karkace karas dinki ki wanke da pea ki dora su su dan dahu ki riga lemun tsami a cikinsu idan ya dahu ki tsiyaye ki aje a gefe

  4. 4

    Sai a jajjaga kayan miya a gefe dankalin a yanka rawun ko na dahuwa da dan kauri a aje

  5. 5

    Idan kayan cikin sun dan dauko dahuwa, sai a zube a saka man gyada kadan a sossoya kayan miyannan sama sama

  6. 6

    Sai ki juye kayan cikin da ruwan duka a cikin soyayyen kayan miyan idan ruwan ba zasu daga shiba a qara kadan

  7. 7

    A zuba kayan dandano, idan ya kusa dahuwa sai a zuba dankalin nan da su karas da aka dafa kadan, idan an kusa saukewa a saka kori.

  8. 8

    Aci hakanan ko da shinkafa.

Edit recipe
See report
Share
Cook Today
Hauwa Bunza
Hauwa Bunza @Hauwabz09
on
Sokoto

Comments

Similar Recipes