Kayan aiki

  1. 2 cupsflour
  2. 1/2tablespoon of salt
  3. 3tablespoons oil
  4. 1 cupwater or as required
  5. Filling
  6. 1/4 gbeef
  7. 1carrot
  8. 1onion
  9. 1tablespoon spices
  10. 2tablespoons oil
  11. 2seasoning cubes or to taste

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Za ki fara da filling. Ki zuba mai a pan idan ya yi zafi, sai ki zuba albasa ki dan soya sama sama. Ki zuba nikakken nama, kayan kamshi da dandano. Ki zuba makimancin ruwa sannan ki rufe. Idan ya kusa dahuwa sai ki zuba grated carrots da tarugu ki rage wuta.

  2. 2

    Ga shi nan bayan na gama. Sai ki rufe ki ajje a gefe.

  3. 3

    Ki zuba flour a bowl. Ki zuba gishiri da mai

  4. 4

    Ki sa hannunki ki mummurje man duka.

  5. 5

    Ki zuba ruwa sannan ki murje

  6. 6

    Ki hada soft dough. Sai ki rufe ki aje shi ya yi resting kamar na minti sha biyar zuwa ashirin.

  7. 7

    Ki dauko dough din sai ki yanka shi guda shida.

  8. 8

    Ga shi nan sai ki dan bubbuda shi kamar haka, ki kokarta saita fadinsu ya zama duk iri daya.

  9. 9

    Ki yi dusting rolling board da flour sannan ki dauko dough guda daya ki shafe shi da mai. Ki tabbatar ya shiga sosai.

  10. 10

    Ga shi nan guda daya duka ya samu

  11. 11

    Sai ki qara dauko wani ki shafa, ki kifa a kan wancan dayan, samanshi ma ki shafa man, da haka har ki yi guda hudu.

  12. 12

    Ki yita murzawa sosai har sai ya yi fadi sosai yayi fyalen fyalen

  13. 13

    Ki dora a bisa non stick frying pan da wuta kadan. Idan dayan gefen ya gasu sai ki juya wani gefen. Haka za ki ma sauran ma

  14. 14

    Ki sauke ki dora a kan rolling board din

  15. 15

    Sai ki nemi plate ko wani abu mai fadi ki yanka kamar yanda yake a hoto. Ki cire duk excess flour din ya gama amfani

  16. 16

    Ga shi nan yanda ya yi

  17. 17

    Ki nemi wuka mai kaifi ki yanka shi gida hudu kamar yanda ya zo

  18. 18

    Sai ki barshi ya huce. Daga nan ki bi a hankali kina rabawa, sai kin nutsu sosai don kar ya lalace. (Shiyasa ake so a zuba wadataccen mai a wurin yi don idan bai ji ba duk zai like a nan)

  19. 19

    Ga shi nan bayan na gama. Daga nan sai ki dama flour da ruwa ba mai yawa ba.

  20. 20

    Sai ki dauko gefe guda ki shafa flour da kika dama, ki dauko dayan gefen ki hade sosai yanda ba zai tashi ba, ki zuba filling din

  21. 21

    Bayan kin zuba, sai ki sake lakuto damammiyar flour ki shafe a sama

  22. 22

    Ki like shi kamar yanda kika yi a farko yanda ba zai tashi bah

  23. 23

    Ga shi nan duka na gama

  24. 24

    Sai a soya a cikin mai.

  25. 25

    Ga yanda cikinsa yayi nan

  26. 26
  27. 27
Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Princess Amrah
Princess Amrah @Amrahskitchen98
rannar
Kaduna
I absolutely love cooking. I can merrily state that my kitchen is my playground in every sense! My mother has always been a wonderful cook, and I feel she is my inspiration.
Kara karantawa

sharhai (8)

Amina Sidi (Mrs)
Amina Sidi (Mrs) @AminaSidi123
Masha Allah, sister kinyi bayani dalla-dalla, jazakillahu Khairan, 👌👌👌💖

Similar Recipes