Potatoes Masa 💯😋

Ummu Sulaymah
Ummu Sulaymah @Sulaymah
Jigawa State

Wannan Masar dankalin munji dadin ta matuqa ni da iyali nah. Abin burgewa kuma shine abinci ne mai qosarwa da kuma lpy 🤗kiyi qoqari ki gwada Er uwah don kiji mi mukaji muma😜🤭#Holidayspecial

Read more
Edit recipe
See report
Share

Ingredients

  1. Dankali manya guda biyar
  2. Kwarai guda biyar manha
  3. Albasa jajjage
  4. Tarugu jajjage
  5. Maggie biyu
  6. Curry rabin qaramin cokali
  7. Black pepper kadan
  8. Powdered garlic
  9. Gishiri
  10. Mai

Cooking Instructions

  1. 1

    Da farko zaki fere dankalin ki sai ki rarraba shi into cubes sai ki zuba a tukunya ki kawo ruwa ki zuba a kai da gishiri kisa bisa wuta ki barshi tsawon minti 5.

  2. 2

    Daga nan sai ki tsame ki zuba a matsami ki barshi yh tsame. Gashi kamar haka

  3. 3

    Sai ki fasa Kwai a bowl ki zuba Maggie, curry, Powdered garlic nd black pepper ki kada sosai

  4. 4

    Sai ki kawo jajjagen albasa da tarugu ki zuba a kai

  5. 5

    Sai ki dauko dankalin ki zuba a kai ki juya ko ina yh shiga ciki kamar haka

  6. 6

    Sai ki dauko masa pan ki daura bisa wuta ki zuba mai ko wane gida ki bare yayi zafi

  7. 7

    Sai nasa ludayi na riqa diba hadin ina zubawa a kowa ne gida na rage wuta na barshi yh nuna a hankali

  8. 8

    Bayan na tabbatar cikin yh nuna sai na juya daya side in Shima yh nuna a hankali

  9. 9

    A haka zakiyi har ki gama

  10. 10

    Ga yanda Potatoes Masa nah yh fito💯😋

  11. 11

    A gsky Er uwah ki gwada wannan Masar dankalin zaki bani labari💯😍💯

  12. 12

    Ga yanda cikin yayi Shima pha hajia tah😘

Reactions

Edit recipe
See report
Share
Cook Today
Ummu Sulaymah
Ummu Sulaymah @Sulaymah
on
Jigawa State
Tasty food is what I love cooking and sharing with my family and friends. Believe in yourself if I can do it you can do it better.🤗
Read more

Similar Recipes