Wainar flour me kifi

Aysher Babangida (Ayshert Cuisines)
Aysher Babangida (Ayshert Cuisines) @cook_24704404
Kano

#mothersday wannan wainar tanada matukar dadi irinta ce ake cewa ba'a bawa yaro me kuya 😂.

Wainar flour me kifi

#mothersday wannan wainar tanada matukar dadi irinta ce ake cewa ba'a bawa yaro me kuya 😂.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Flour
  2. Attaruhu
  3. Albasa
  4. Maggi
  5. Gishiri
  6. Sosayyen kifi
  7. Kwai
  8. Manja

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Zaki gyara attaruhu da Albasa sai ki wanke ki yanka albasa kanana ki jajjaga attaruhu.

  2. 2

    Zaki gyara kifin ki sai ki cire kayar dake cikin shi.

  3. 3

    Zaki tankade flour acikin kwano me kyau sai ki zuba maggi da gishiri sai ki juya sai ki zuba ruwa ki kwaba sai ki kawo attaruhu da albasa da kifi ki zuba aciki sai ki fasa kwai acikin wani kwano daban sai ki kada sosai sai ki juye acikin kullun ki sai ki juya.

  4. 4

    Zaki daura kasko akan wuta sai ki barshi yayi zafi sai ki dakko manja ki zuba kadan aciki sai ki dakko kullun ki zuba aciki sai ki barta ta soyu idan tayi sai ki juya daya gefen shima ya soyu haka zakiyita yi har ki gama sai kici da yaji.

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Aysher Babangida (Ayshert Cuisines)
rannar
Kano

sharhai

Similar Recipes