Farar taliyar noodles da miyar tumatir,albasa da kifin gwangwani

Masu dafa abinci 100+ sun ziyarci wannan girkin
Askab Kitchen
Askab Kitchen @askab24617

#oneafrica wannan girki ne mai matukar dadi gashi kuma baya daukar lokaci wajen hadawa. Iyalina suna matukar jin dadinsa.

Kara karantawa
Gyara girkin
See report
Tura

Kayan aiki

goma
mutane biyu
  1. Taliyar noodle guda Biyu
  2. Tumatir manya guda Biyu
  3. Albasa babba guda Daya
  4. Attaruhu, tafarnuwa da danyar citta
  5. Sinadarin dandano nacikin taliyar noodle din
  6. Kayan kamshi
  7. Mai cokali Uku
  8. Kifin gwangwani guda daya

Umarnin dafa abinci

goma
  1. 1

    Dafarko za'a dora ruwa a tukunya adora akan wuta, sai a barshi ya tafasa sannan azuba taliyar noodles din azuba mai cokali daya, abata minti uku ta dahu sai a tace a mataci a ajiye a gefe.

  2. 2

    A Daura kaskon yin miya a akan wuta a zuba mai cokali biyu sannan azuba albasa a barta ta soyu na minti biyu, sai a zuba jajjagagen attaruhu da albasa wanda aka hada da tafarnuwa da danyar citta aka jajjaga. Azuba yankakken tumatir asoya sannan azuba kayan kamshi, azuba sinadarin dandano na cikin taliyar noodles din. A dauko kifin gwangwani a tsiyaye man ciki Sai a zuba kifin a cikin miyar a jujjuya, a rufe abashi minti biyu zuwa uku komai ya dahu sai sauke.

  3. 3

    Asamu mazubi mai kyau azuba wannan farar taliyar noodles din a gefe sannan a zuba wannan miyar tumatir da albasa da kifin gwangwani akai.
    #oneafrica

Yanayi

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan

sharhai

Wanda aka rubuta daga

Askab Kitchen
Askab Kitchen @askab24617
rannar

Similar Recipes

More Recommended Recipes