Sauce din Hanta me sauki

Afrah's kitchen
Afrah's kitchen @Afrah123
Kano

Yana da dadi sannan kuma yana kara lafiya

Sauce din Hanta me sauki

Masu dafa abinci 8 suna shirin yin wannan

Yana da dadi sannan kuma yana kara lafiya

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Hanta
  2. Albasa babba daya
  3. Attaruhu uku
  4. Tattasai daya babba
  5. Tumatir uku
  6. Kayan kamshi
  7. Citta danya
  8. Maggi biyu
  9. cokaliOnga karamin
  10. Curry na gari cokali daya karami
  11. Mai cokali uku

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Zaki wanke hanta ki yankata kanana sae ki saka mai a kasko mara kamu kisa Albasa kadan in yayi zafi ki zuba hanta ki soyata sama sama. Ki zuba maggi,kayan kamshi,citta danya,curry,onga da maggi Sannan ki yanka albasa ki zuba yayi kamar minti uku.

  2. 2

    Ki zuba yankakken tattasai da attaruhu ki juya. Ki barshi yayi minti biyar.

  3. 3

    Sannan ki kawo tumatir da kika yanka ki zuba ki juyashi ki rufe da murfi.

  4. 4

    Gashi angama, zaki iya ci da farar shinkafa,doya,dankali,ko taliya ko couscous

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Afrah's kitchen
rannar
Kano
cooking is my fav
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes