Tura

Kayan aiki

Awa daya
mutane uku
  1. Tsakin masara gwangwani biyu
  2. Kayan miya tattasai(3),attarugu(5),tumatur (5)albasa,(2)
  3. yankaKabewa (6)
  4. Alaiyahu ba mai yawa ba sosai
  5. Gyada gwangwani daya
  6. Wake gwangwani daya
  7. Mai (3) table spoon
  8. Maggi (3)
  9. Gishiri (1) teaspoon
  10. Kayan kamshi (1) cokalin shayi daya
  11. Ounga(1) leda
  12. Gino curry (1) leda

Umarnin dafa abinci

Awa daya
  1. 1

    Da farko,agyara wake a wanke sai adora shi a wuta ya dahu sai atace a ajiye gefe.

  2. 2

    Sai a wanke gyara kayan miya a wanke ayi blending tare da kabewa bayan an wanke ta itama

  3. 3

    Sai a Dora tukunya a wuta asa mai in yayi zafi a zuba kayan miyan nan su soyu,sai a tsayar da ruwa da dan yawa ruwan ake so a zuba Maggi da gishiri a rufe ya tafasa

  4. 4

    Sai a kawo waken nan a zuba tare da gyadar da aka nika amman bada laushi sosai ba,a wanke tsakin masarar shima sosai,

  5. 5

    Sai a zuba ayi ta juyawa sai Ya hade tare da waken,sai akawo su ounga da Gino a zuba,arufe a barshi ya dahu

  6. 6

    ,in ya nuna sai a zuba yankakkiyar albasa tare da alaiyahun da aka gyara aka yanka a rufe tukunyar kashe wutar zafin zai nunar da alaiyahun.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Ummu Khausar Kitchen
rannar
Kano
girki adon mace ina son girki mussaman namu na gargajiya.
Kara karantawa

Similar Recipes