Tura

Kayan aiki

1hr 30mnt
3 yawan abinchi
  1. Fulawa kofi biyu
  2. Albasa babba guda daya
  3. ,Attaruhu manya guda hudu
  4. Mai dandano guda hudu
  5. Sai manja rabin kofi
  6. Tafarnuwa guda 2 matsakaita

Umarnin dafa abinci

1hr 30mnt
  1. 1

    Da farko na samu mazubi Mai kyau n tankade fulawa ta a ciki,sannan na daka me dandano na zuba,

  2. 2

    Na jajjaga attaruhu da Tafarnuwa n zuba akan fulawa ta na zuba ruwa dae dae yanda zai kwaba min kullin wainata,

  3. 3

    Kwabin yayi daidai misali kar yayi ruwa sosai Kuma kar yayi kauri sosai

  4. 4

    Sannan n zuba manja daidai yanda nake so ya dau zafi sannan n sake juya kullin wainata na fara diba ina soya ta idan daya bangaren y soyu saina juya daya bangaran shima y soyu

  5. 5

    Saina kwashe n Kuma zuba wata har n gama soyawa n samu faranti n Mai kyau n zuba t a ciki na sa yaji n a gefe shikenan n gama wainar fulawa.

  6. 6

    Shike nan saina dakko kaskon suya ta na kunna wuta na dora kasko n na ya fara daukan zafi

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Hygienic Snacks and Spices kn
rannar
I love cooking and making snacks
Kara karantawa

sharhai (2)

Jamila Ibrahim Tunau
Jamila Ibrahim Tunau @Jamitunau
Kai kai kai bari in dauko ruwan sanyi kusa

Similar Recipes