Dan waken fulawa

Yar Mama
Yar Mama @YarMama
Bauchi

Shi danwake na da farin jini a wajen masu son shi idan aka mishi hadi na daban yana dadi sosai.#Suhurrecipecontest

Dan waken fulawa

Mai dafa abinci 1 yana shirin yin wannan

Shi danwake na da farin jini a wajen masu son shi idan aka mishi hadi na daban yana dadi sosai.#Suhurrecipecontest

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

60mintuna
3 yawan abinchi
  1. Fulawa gwangwani hudu
  2. Garin kuka cokali biyu
  3. Ruwan kanwa cokali takwas
  4. gwangwaniManja rabin
  5. Albasa manya biyu
  6. Attarugu guda hudu
  7. Kwai guda hudu
  8. Tafanwa biyu
  9. Dunkule hudu

Umarnin dafa abinci

60mintuna
  1. 1

    Farko zaki tankade garin fulawa a ruba mai da zurfi da fadi ki tankade kuka akai sai ki zuba ruwan kanwa sai ki kara zuba ruwa kina gaurayawa kina chakudawa kina mutsukawa har ya hada jikinshi yanda zaki iya gutsira da hanu kar ki cika ruwa kuma kar yayi karfi sosai.

  2. 2

    Ki samu tukunya mai fadi ki zuba ruwa a ciki ki daura a wuta idan ya tafasa sai ki zo kina gutsiran kwabin nan naki kina wurgawa ciki har ki gama sai ki rufe ki zauuna kusa don idan ya tafasa zai zuba idan baa bude ba. Idan ya tafasa ya juya sai a kwashe a cikin ruwan sanyi.

  3. 3

    Zaki sa tukunya a wuta kisa manja sai ki yanka albasa akai ki jajjaga attarugu da albasa ku zuba akai ki sa kayan kamshi dana dandano sai ki soya.

  4. 4

    Zaki dafa kwai ki bare sai ki yanka su.

  5. 5

    Ki samu plate ki zuba danwake sai ki zuba yar miyar ki sai ki jera kwai sai aci dadi lafiya.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Yar Mama
Yar Mama @YarMama
rannar
Bauchi
Kitchen is my favorite place
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes