Tuwon shinkafa da miyar taushe

Fatima Bint Galadima
Fatima Bint Galadima @Homechef2000
Kano State

#sahurrecipecontest tuwon shinkafa da miyan taushe yanada matuqar Dadi abincine Wanda idan kaci baza kaji yunwa da wuriba Kuma bayasa mutum yawan Shan ruwa Yana qara lpy ajiki saboda ya qunshi abubuwa da dama acikinsa Shi yasa nida iyalina muke matuqar son Shi a matsayin abincin sahur Yana da matuqar Dadi da amfani a jikin mutum idan Kun gwada zakuji dadinshi sosae

Tuwon shinkafa da miyar taushe

Masu dafa abinci 2 suna shirin yin wannan

#sahurrecipecontest tuwon shinkafa da miyan taushe yanada matuqar Dadi abincine Wanda idan kaci baza kaji yunwa da wuriba Kuma bayasa mutum yawan Shan ruwa Yana qara lpy ajiki saboda ya qunshi abubuwa da dama acikinsa Shi yasa nida iyalina muke matuqar son Shi a matsayin abincin sahur Yana da matuqar Dadi da amfani a jikin mutum idan Kun gwada zakuji dadinshi sosae

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

awa daya
mutum uku
  1. Shinkafa Kofi biyu ta tuwo
  2. Gyada rabin kofi
  3. Man gyada rabin kofi
  4. Timatir manya guda biyar
  5. Tattasai manya guda uku
  6. Attaruhu guda biyu
  7. Albasa babba guda daya
  8. Nama
  9. Sinadarin dandano guda biyar

Umarnin dafa abinci

awa daya
  1. 1

    Ga Kayan da nake buqata

  2. 2

    Da farko Zaki jiqa shinkafar ki tayi minti goma sae ki wanke ta ki zuba a tukunya ruwa ya Haye kanta sae ki rufe ta idan ta Fara tafasa ki rage wutarki ki barta ta tso tse a hankali idan ta tso tse sae ki tuqa ta sosae ki dakko Mara da qoqo ki malmala sae kisa a flask

  3. 3

    Ita Kuma miyar taushe da farko Zaki wanke Kayan miyanki ki markada sae ki zuba a tukunya ki tafasa namanki ki ajiye Shi ki dora wannan Kayan Miya a wuta idan ya tafasa ya tso tse kisa namanki akai ki zuba man gyada ki soya su idan ya soyu sae ki zuba sinadarin dandano akai ki zuba gyadarki akai ki kawo ruwan namanki ki zuba ki kawo wankakken alayyahunki Wanda Kika yanka ki zuba akae sae ki juya su sannan ki rufe idan yayi minti uku sae ki sauke

  4. 4

    Shikenan tuwon shinkafa miyar taushe ya kammala ayi sahur cikin nishadi da walwala

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Fatima Bint Galadima
Fatima Bint Galadima @Homechef2000
rannar
Kano State
I love cooking infact cooking is mah hobby I can spend all the day in kitchen without worrying my kitchen my pride!!!
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes