Tura

Kayan aiki

20minti
2 yawan abinchi
  1. Tsaki gwangwani 1 da rabi
  2. Alayyaho yawan da kake so
  3. Attaruhu 3
  4. albasa 1 medium
  5. Maggi 2
  6. gishiri kadan
  7. kitse

Umarnin dafa abinci

20minti
  1. 1

    Da farko na gyara tsaki na na wanke shi tas

  2. 2

    Na jajjaga attaruhu da albasa na dora tukunya da ruwa a ciki na zuba jajjagen na kawo maggi da gishiri na zuba to taste

  3. 3

    Na zuba kitse na gauraya na barshi ya tafasa bayn ya tafasa na dauko wankakken tsaki na na zuba na gauraya barshi na dan mintuna

  4. 4

    Kafin nan na yanka alayyaho na wanke shi tas bana saka yakuwa sbd bana son tsami yana tayar mn da ulcer amma in kina so zaki iya sakawa ko rama

  5. 5

    Na barshi ya turara na sauke aci dadi lapia

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Hafsatmudi
Hafsatmudi @Hafsatmah08
rannar
Bauchi

Similar Recipes