Faten Shinkafa Da wake

Jamila Hassan Hazo
Jamila Hassan Hazo @Jermeelerh2

Nayi Kunun Gari Basise Sai sauran dafaffiyar shinkafa wacce taji gyada da Kanumfari da citta tayi saura 😚nikuma banison inzubar sainace mezai hana inyi fate dashi?🤔 kuma tunda gyadar cikin dafaffiyar shinkafar markadeddiyace kunga basai nasake zuba gudajin gyada ba, ina bude firji kawai sainaga inada sauran wakena dafaffiya sai nace barin gwada sabuwar samfurin fate hmmmmmmmm megida yayi santi ba kadanba 😍😋😋😜
#gargajiya

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

mintuna 20mintu
Daya
  1. Dafaffiyar farar shinkafa
  2. Kanumfari
  3. Citta
  4. Dafaffiyar wake
  5. Ganyen albasa da gudajin albasa (yankakku)
  6. Alayyaho(yankakke)
  7. Jajjagen tattasai da attarugu
  8. Maggi
  9. Gishiri kadan
  10. Manja
  11. Tafarnuwa

Umarnin dafa abinci

mintuna 20mintu
  1. 1

    Zuba manja atukunya dake kanwuta intafara soyuwa sai a kawo jajjagen tattasai da attarugu azuba

  2. 2

    Yita juyawa harsaiya soyu sai azuba ruwa cup daya da rabi sai arufeshi yafara tafasa

  3. 3

    Adaka tafarnuwa azuba a tafasashen ruwan sanwar

  4. 4

    Zuba dafaffiyar shinkafar dake hade da markadedden gyada da Kanumfari da citta

  5. 5

    Azuba maggi da gishiri akuma zuba dafaffiyar wake arufe yasake tafasa na minti 5

  6. 6

    Akawo wankakkiyar alayyaho da ganyen albasa da gudajin albasar sai arufe minti daya asauqe daga kanwuta

  7. 7

    Kar abude tukunyar sai bayan minti 5

  8. 8

    Aci dadi Lafiya

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Jamila Hassan Hazo
rannar
I Drive Pleasure While Cooking
Kara karantawa

sharhai (6)

Similar Recipes