Faten tsaki

Ruqayyah Anchau
Ruqayyah Anchau @anchau_cooks
Kaduna

A garinmu ana yawan yin pate sosai duk sha'ani sai anyi shi, shiyasa nima nake san pate

Faten tsaki

Masu dafa abinci 2 suna shirin yin wannan

A garinmu ana yawan yin pate sosai duk sha'ani sai anyi shi, shiyasa nima nake san pate

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Tsakin masara
  2. Dafaffen wake
  3. Gyada
  4. Kayan miya
  5. Alaiyahu
  6. Mangyada
  7. Maggi da gishiri
  8. Kayan kamshi

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko zaki wanke tsakin ki tas ki aje a gefe, sai ki yanka alaiyahunki ki wanke shima ki aje a gefe, sai ki dan daka gyadarki shima ki aje a gefe

  2. 2

    Ki dora tukunya a wuta sai kisa mangyada ki soya markaden kayan miyanki anya soyu dai ki zuba maggi, gishiri, kayan kamshi sai ki tsaida sanwa, sai ki dakko gyadar nan kisa su tafaso tare

  3. 3

    Bayan ya tafasa sai ki zuba tsakinki kina juya kiyita juyawa har yayi kauri sabida kar ya kwanta a kasa. In yayi kauri sai ki barshi ya dahu. Daganan sai ki zuba dafaffen waken ki Kafin ya gama dahuwan sai ki zuba alaiyahunki ki barshi na mintuna biyar. Shikenan kin gama paten tsakin ki

  4. 4

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Ruqayyah Anchau
Ruqayyah Anchau @anchau_cooks
rannar
Kaduna
Welcome to my world of cooking ❤️😍😘💕♥️
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes