Miyar kayan lambu

Na san ba ni na fara yin irin miyar nan ba, amma dalilina na qirqirarshi a kan kaina saboda Babana ne, yana son cous cous da miyar kayan lambu, alayyahu ne ko dai ko wane irin ganye, to wannan miyar dominshi na yi musamman.
Maganar gaskiya kuma sinadarin dandano da na yi amfani da shi a wannan miyar ita ce zan ce kusan sirrin fito da dandanon wnn miyar, mun ci miyar tare da dafaffen cous cous.
Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko za a yayyanka kayan lambu fasalin da ake so, Sai a zuba mai cikin tukunya a daura kan wuta in ya yi zafi a zuba albasa ana juyawa zuwa minti daya da rabi sai a juye niqaqqen attaruhu da citta da tafarnuwa a siya na minti biyu,
- 2
Sai a kawo tumatur a zuba a saka sinadarin dandano a juya sai kuma soyayyar kaza
- 3
A zuba curry a juya, bayan mintuna biyar sai a zuba karas da yalo
- 4
Sai a zuba ruwan nama a dama corn flour da ruwa cokali daya a zuba, a zuba cauliflower da aka yayyanka aka wanke
- 5
Sai a zuba tattasai tare da kabeji a juya a rufe bayan an yi qasa da wuta na tsahon minti biyar sai a kashe wuta. Shi kenan.
Cooksnaps
Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!
Wanda aka rubuta daga
Similar Recipes

Butter chicken


Gasasshen kifi da miyar kayan lambu


Shinkafa mai kayan lambu da miyar dankali da nama


Soyayyiyar shinkafa da lemon mangwaro


Taliya da miyar kayan lambu


Sauce din kayan lambu da cabbage


Tuwon semo miyar kuka


Faten doya


Shredded beef sauce


Soyayyiyar Kaza


Gasashshen naman sa mai kayan lambu


Miyar dankali da karas


Farantin dankali


Dambun cous cous da zogale


Farar shinkafa da miyar kayan lambu


Bhindi masala(miyar kubewa)


Soyayyiyar shinkafa, kaza mai yaji da hadin koslo/(coleslaw)


Stir fry cous cous


Alkubus na flour


Girgijen madara na dabino da inibi


Hadadden burodi


Sauces en kayan lambu da nama


Miyan alayyahu da naman kaza


Peppe chicken


Cous cous da wake da miyan alayyahu


Chocolate da red velvet cake


Miyar dankali da kayan lambu


Shredded liver sauce


Blue hawaii


Alala Mai kayan lambu

sharhai (7)