Miyar dankali da karas

TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA)
TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA) @cook_15480513
Port Harcourt

Hhhmmm wannan miyar tayi dadi sosai. 💃💃💃😋😋

Miyar dankali da karas

Masu dafa abinci 4 suna shirin yin wannan

Hhhmmm wannan miyar tayi dadi sosai. 💃💃💃😋😋

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Dankalin turawa guda hudu
  2. Karas manya guda biyu
  3. Albasa babba daya
  4. Attarugu
  5. Tafarnuwa
  6. Mai
  7. Maggi da sauran kayan dandano
  8. Curry da thyme
  9. Naman kaza ko na rago
  10. Corn flour chokali daya

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Dafarko natafasa namar kazata da kayan kanshi nabarshi yatafasa sosai har yashanye ruwan kuma yanuna. Sai nasauke na ajiye agefe. Bayannan sai nadaura tukunyar da zanyi miyar da ita a wuta nazuba mai dayayi zafi sai nazuba albasa da karas nasoyasu zuwa minti biyar sai nazuba jajjagen attarugu da tafarnuwa najujjuya sai nazuba maggi curry dasauran sinadaran girki. Sai nazuba tafasasshen dankalina akai sai nazuba ruwa daidan yanda zai isa miyata sai nazuba nama narufeta don yatafasa

  2. 2

    Bayan yatafasa sai nadama corn flour dina nakada akan miyar donyayi kauri. Sai narufe tukunyar nakuma rage wutan nabarshi zuwa minti uku sai nasauke.

  3. 3

    Wannan miyar tanada dadi sosai kuma zaki iya cinta da shinkafa taliya macaroni ko kuskus

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA)
rannar
Port Harcourt
Gskiya arayuwata inason girki sosai shiyasa kullum ina kicin wurin tsara abinci kalakala
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes