Butter chicken

Afaafy's Kitchen
Afaafy's Kitchen @mohana10
Kano

Wannan girki ya samo asali ne daga arewacin qasar hindu tun wajejen shekarun 1950s. Manyan kayan hadinshi shi ne kaza,butter da tumatur, sauran duk qari ne dan fito da dandano na musamman.
Na yi wannan girki ne domin kaina. Na tashi tun ina yarinya dalilin kallon fina-finansu na fara sha'awar al'adunsu, yarukansu da abincinsu, wannan yana daya daga cikin abincinsu da nake matuqar so.

Kara karantawa
Gyara girkin
See report
Tura

Kayan aiki

hr 2mintuna
4 yawan abinchi
  1. Kilon kaza
  2. Tumatur guda hudu
  3. Tumatur na leda (rabin kofi)
  4. Albasa guda daya babba
  5. Attaruhu guda uku
  6. 6Qwallon cashew guda
  7. Butter kofi daya
  8. Sinadarin dandano
  9. Chicken masala
  10. Garin paprika
  11. Garin coriander
  12. Garam masala
  13. Kofi daya na cooking cream
  14. Don tsuma kaza
  15. Yoghurt rabin kofi
  16. Niqaqqen hadin danyar citta,tafarnuwa da parsley
  17. Cumin da habba qaramin cokali daya
  18. cokaliChicken masala qaramin
  19. cokaliGarin paprika qaramin
  20. cokaliTandoori masala qaramin
  21. cokaliGaram masala qaramin
  22. Sinadarin dandano
  23. Lemon tsami cokali daya

Umarnin dafa abinci

hr 2mintuna
  1. 1

    Farko za a wanke kaza da kyau a tsane ruwan da ke jiki, sai a zuba a kwano mai dan zurfi a zuba duk kayan da na ambata a sashen tsuma kaza, sai a cakude komai ya hada jikinshi, a ajiye a gefe a bashi awa daya ya tsumu.

  2. 2

    Bayan nan sai a zuba butter a cikin kasko, a juye tsumammiyar kaza a kai a dafa shi, (zai saki ruwa,ruwan shi zai dafa kazar)a jira har ya tsotse tas ya saki mai a dan qara soya shi sama sama, sai a kwashe a ajiye a wani kwanon a gefe.

  3. 3

    A cikin kaskon a qara wani butter a zuba albasa a soya na minti daya, sai a saka attaruhu guda guda da spices din.

  4. 4

    A juya, a zuba yankakken tumatur a qara soyawa na minti biyu,sai a saka qwallayen cashew da sinadarin dandano, a zuba ruwa cokali biyu a barshi ya dahu na minti 8, sai kashe wuta a barshi ya dan huce sai a juye a blender a markada ya yi laushi

  5. 5

    Daga nan sai a qara juyewa cikin kaskon a zuba tumatur din gwangwani da ruwa don rage kaurinshi(idan ba a zuba wajen markaden ba,sannan wasu suna tace markaden sbd tsakin qwallon cashew),

  6. 6

    A qara chicken masala da garam masala a juya a zuba soyayyar kaza da aka ajiye a dafa na minti 10, bayan nan sai a zuba cream a rage wuta bayan minti biyar sai ka kashe duka

  7. 7

    Sai a juye sauran butter ciki a juya a zuba yankakken parsley a sama,shi kenan.

    Na ci nawa da roti, ya yi dadi sosai. Za a iya ci da shinkafa ma ko cous cous

Yanayi

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan

Wanda aka rubuta daga

Afaafy's Kitchen
rannar
Kano

Similar Recipes

More Recommended Recipes