Chicken Shawarma

Meenat Kitchen
Meenat Kitchen @meenat2325
Kano State

#SHAWARMA. Iyalaina sunji dadin vegetables shawarma shiyasa yauma nayi masu amma saina canja musu nasa naman kaza aciki domin jin dadinsu, idan nace zansake yimusu vegetables shawarma ba lallai bane ta kayatar dasu amma canjin yanayin abinchi a iyali yanasa koda yaushe su dunga dokin cinsa.

Chicken Shawarma

#SHAWARMA. Iyalaina sunji dadin vegetables shawarma shiyasa yauma nayi masu amma saina canja musu nasa naman kaza aciki domin jin dadinsu, idan nace zansake yimusu vegetables shawarma ba lallai bane ta kayatar dasu amma canjin yanayin abinchi a iyali yanasa koda yaushe su dunga dokin cinsa.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

awa 1mintuna
2 yawan abinchi
  1. bangaren biredin shawarma
  2. Kofi biyu da rabi na flour
  3. Babban cokali daya na yeast
  4. Kofi daya na ruwan dumi
  5. Karamin cokali daya na gishiri
  6. Babban cokali daya na sukari
  7. Babban cokali daya na mai
  8. bangaren kayan cikin shawarman
  9. Kirjin kaza daya
  10. 1/4 tspthyme
  11. 1/4na garin tafarnuwa
  12. 1/4na gishiri
  13. Sinadarin dandano guda biyu
  14. bangaren hadin mayonnaise
  15. 1 tbsHot chili sauce
  16. 1 tbsgarlic& chili sauce
  17. 2chili mayonnaise
  18. 1 tbsketchup

Umarnin dafa abinci

awa 1mintuna
  1. 1

    Wanann sune kayan danake bukata alokacin hada pita bread (wato biredin shawarma)

  2. 2

    Dafarko zaki samu babban bowl ki zuba flour dinki kisa gishiri,sugar,yeast da mai

  3. 3

    Saiki jujjuyasu da hannunki koda wooding spoon

  4. 4

    Saikisa ruwanki mai dumi ki kwaba

  5. 5

    Saiki maidashi kan chopping board ko gurin da kike murza flour kiyita murzawa na mintuna 5 zakiga yadaina kama hannunki kuma yayi kyau a ido

  6. 6

    Saiki shafawa bowl dinki mai ki maida dough dinki ciki kisa kitchen towel ki rufe kisa a guri mai dumi zakiga ya tashi yayi double din size dinsa

  7. 7

    Bayan yatashi din nan saiki daukosa kiyi pushing dinsa iska ta fita saiki rabashi guda 10

  8. 8

    Saiki dauko daya bayan daya ki muzashi da fadi kamar haka Idan kin gama kisa a tray kibashi mintuna 10-15 saiki gasa

  9. 9

    Saiki dauko fry pan kisa a wuta idan yayi zafi kisa ki gasa kowanne bangare kamar haka saiki kwashe ki samu kitchen towel kisa a ciki hakane zai bashi damar yin taushi idan kunzo ci

  10. 10

    Wannan kayan sune muke bukata alokacin hada kayan cikin shawarma

  11. 11

    Da farko zaki samu tsokar kirjin kaza ki yankata kananu saiki zuba a fry pan ki jajjaga attarugu ki zuba ki zuba yankakken tattasai kisa sinadarin dandano,thyme,garlic powder da mai

  12. 12

    Saikisa albasa da Korean tattasai kibashi mintuna 10-15 saiki sauke

  13. 13

    Saiki dauko bowl karami kisa mayonnaise, chili sauce,garlic & chili sauce sai ketchup ki juyasu

  14. 14

    Saiki shafawa biredinki na shawarma saiki zuba hadin namanki da kabeji in kinaso kenan saiki nade

  15. 15

    Shikenan kin gama hada chicken shawarma

  16. 16
  17. 17
Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Meenat Kitchen
Meenat Kitchen @meenat2325
rannar
Kano State
my name is Amina Mohd Sani, cooking is my fev,cooking is my hubby......
Kara karantawa

sharhai (4)

Ayshat Adamawa(U. Maduwa)
Ayshat Adamawa(U. Maduwa) @Ayshat_Maduwa65
@cook_14221390 daughter kinyi wuyan gani kwana biyu

Similar Recipes