Fettuccine16 Jallof

Afaafy's Kitchen
Afaafy's Kitchen @mohana10
Kano

😂karon farko knn da na fara ganin irin taliyar nan,farko na tsayq jajantawa kaina daga baya kuma na saki jiki da ita har na shirya wannan daddadan girkin,dadi ba a mgn🤗

Fettuccine16 Jallof

Mai dafa abinci 1 yana shirin yin wannan

😂karon farko knn da na fara ganin irin taliyar nan,farko na tsayq jajantawa kaina daga baya kuma na saki jiki da ita har na shirya wannan daddadan girkin,dadi ba a mgn🤗

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

30 minutes
3 yawan abinchi
  1. Taliyar fettuccine16 guda daya
  2. Karas a yanka shi a tsaye rabin kofi
  3. Koren wake rabin kofi
  4. Albasa
  5. Attaruhu
  6. Tumaturin leda daya
  7. Nama a yankashi a tsaye rabin kilo
  8. cokaliGarrin curry mai girfa rqbin
  9. Garin citta da tafarnuwa rqbin cokali
  10. Koren tattasai da jan tattasai
  11. Sinadarin dandano
  12. Mai

Umarnin dafa abinci

30 minutes
  1. 1

    Da farko zaki fara daura ruwa a kan wuta cikin tukunya mai tsafta ki rufeshi ya tafasa,sai ki dauko taliyar fettuccine dinki ki saka ta a tsaye,da kanshi zai shiga ciki duka,ki juyashi ki rufe,kina yi kina dan dubawq sbd kada ya dunqule,in ya dahu ba da yawa ba ki tace cikin matsamin

  2. 2

    A wata tukunyar daban zaki zuba mai yadda zai isheki,sai ki saka namannan da aka yanka a tsaye,ki kawo garin citta da tafarnuwanki ki saka ki juya,snn ki kawo sinadarin dandanonki ki saka

  3. 3

    Ki saka garin curry mai hade da girfa,ki juya ki barshi na minti uku ya dahu,sai ki kawo albasarki da attaruhu ki zuba,ki juya yayi minti daya sai ki saka tumatirin leda akai ki juya

  4. 4

    Ki barshi na minti daya,ki saka karas dinki da koren wake tare da jan tattasai ki juya

  5. 5

    Sai ki kawo ruwa kamar kofi biyu ki zuba a kai ki barshi ya tafaso,sai ki juye tafasasshiyar taliyarki,ki cakudeshi duka ki rage wuta ki rufe ki bashi minti biyar🤗daga nn sai ci

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Afaafy's Kitchen
rannar
Kano

sharhai

Similar Recipes