Miyan taushe

Amcee's Kitchen
Amcee's Kitchen @Amina69
Zaria,kaduna State

Wannan miya nayishi saboda challenge ne saboda inata tunani me nake dashi wanda ya dade a fridge Sai na tuna inada nikakken kayan miya a freezer yafi 1 month nace bari nayi amfani dashi a challenge hmmm wannan miya duniya ne #OMN

Miyan taushe

Wannan miya nayishi saboda challenge ne saboda inata tunani me nake dashi wanda ya dade a fridge Sai na tuna inada nikakken kayan miya a freezer yafi 1 month nace bari nayi amfani dashi a challenge hmmm wannan miya duniya ne #OMN

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Tumatir
  2. Tarugu
  3. Tattasai
  4. Albasa
  5. Alayyaho
  6. Lawashi
  7. Gyadan miya
  8. Magi
  9. Citta
  10. Tafarnuwa
  11. Mix spices
  12. Masoro
  13. Da cinnamon
  14. Manja
  15. Sai nama

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko zaki gyara tumatir, tarugu, albasa da tattasai,citta da tafarnuwa
    Sai ki wanke ki jajjaga
    Ki samu tukunya ki daura akan wuta Sai kisa manja da albasa ki soya Sai ki zuba kayan miyan ki

  2. 2

    Ki barshi ruwan ya tsotse Sai ki soya idan yayi Sai kisa ruwa kisa kayan kamshi,Magi da gyada
    Zaki gyara gyadan ki daka yayi laushi

  3. 3

    Idan gyadan ya nuna Sai kisa lawashi da nama
    Nidai nayi amfani da naman kaza bayan minti biyar Sai kisa alayyaho ki barshi yayi kaman minti biyu Sai ki sauke

  4. 4

    NOTE
    Idan zaki wanke alayyaho zakisa gishiri kadan Sai ki wanke sosai sannan ki yanka
    Ni ina wanke alayyaho kafin na yanka saboda idan akwai datti ko tsutsa karna yanka dashi

  5. 5

    Aci miyan taushe lafiya naci nawa da tuwan shinkafa

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Amcee's Kitchen
rannar
Zaria,kaduna State
cooking is my fav
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes