Miyar ganye (Vegetable soup)

Ayshat Adamawa(U. Maduwa)
Ayshat Adamawa(U. Maduwa) @Ayshat_Maduwa65
Abuja

#omn Daman inata iru wato daddawan yarbawa a fridge yafi wata hudu banyi anfani dashi ba shine na fidda shi yanzu nayi anfani dashi a wannan challenge din duk abinda nayi anfani dashi a wannan miyan fresh ne. Kamshin miyan nan ba a magana. Wannan na alayyahu kadai nayi zansa Dayan recipe na wadda nayi da ughu leave sai aci da tuwo.

Miyar ganye (Vegetable soup)

Masu dafa abinci 4 suna shirin yin wannan

#omn Daman inata iru wato daddawan yarbawa a fridge yafi wata hudu banyi anfani dashi ba shine na fidda shi yanzu nayi anfani dashi a wannan challenge din duk abinda nayi anfani dashi a wannan miyan fresh ne. Kamshin miyan nan ba a magana. Wannan na alayyahu kadai nayi zansa Dayan recipe na wadda nayi da ughu leave sai aci da tuwo.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

Minti talatin
Mutane uku
  1. Alayyahun dari biyu
  2. Fresh tumatir guda hudu
  3. Manyan albasa guda biyu
  4. Shombo gudu hudu
  5. Iru daddawan yarbawa chokali biyu
  6. Attarugu guda uku irin masu kamshin nan😂
  7. Maggi naija pot, knorr da maggi star nayi anfani
  8. Dan manja da man gyada
  9. Ganda
  10. Nama iya yadda akeso
  11. Kifi yadda ake bukata
  12. Crayfish chokali biyu

Umarnin dafa abinci

Minti talatin
  1. 1

    Da farko zaki yayyanka duk danyen kayan su tumatir,shombo,attarugu,albasa da alayyahu, sai ki ajiyesu a gefe

  2. 2

    Zaki samo tukunyarki mai tsabta ki zuba albasa da mai da manja ki soyasu sama sama

  3. 3

    Ki zuba yakkakken Kayan miyarki zaki iya jajjaga shombo da attarugu dan yana zafi a hannu idan kin yayyanka

  4. 4

    Bayan kin soyasu sama sama sai ki zuba ruwan namanki kadan tare da naman, kifi, Ganda, crayfish sai Kayan dandano. Nidai banasa curry dasu thyme dan banason wannan locally kamshi ya bata

  5. 5

    Daga nan sai ki zuba alayyahun akai ki juya da kyau sai ki barshi for 1 min yayi steaming kawai sai ki kashe

  6. 6

    Zaki iya ci da white rice, tuwon shinkafa, tuwon semo, jollof rice da dai sauran su yana da dadi sosai ga Kara lfy.

  7. 7

    Idan kinaso zaki iyayi da mai kadai ko manja, for daddawan kuMa idan kinaso zaki iya soyawa cikin mai ko kuma sai lokaci da zaki zuba su laman ki sai ki zuba duk yadda kikeso dai.

  8. 8

    Wannan nayi shi ne da ganyen alayyahu kawai Amma akwai wadda nakeyi dasu ughu da waterleave shima zansa nashi recipe din insha Allah. Zaki iya sa duk naman da kike dasu.

  9. 9

    Hakan nan nayi packing din nawa na tafi office dashi wlh tayi dadi sosai

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Ayshat Adamawa(U. Maduwa)
Ayshat Adamawa(U. Maduwa) @Ayshat_Maduwa65
rannar
Abuja
cooking is my dream and also cooking is all about being creative
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes