Ingredients

  1. 4Shinkafa kofi
  2. Yeast cokali babba daya
  3. Sugar rabin kofi
  4. Kanwa in da buqatar kanwa
  5. Mai na suya

Cooking Instructions

  1. 1

    Idan shinkafar ki bata buqatan gyara saiki jiqa ta zuwa awa daya ki wanke sai anmarkada ta da kauri yadda idan kinxo suya zaki iya qara ruwa daidai yadda kike so.

  2. 2

    Bayan ankawo markaden saiki sakata wuri mai dumi ki barta zuwa awa3 saiki dauko ta ki tabbatar yeast dinki active ne saiki zuba yeast din ki mixing kullum sosai, idan lokacin sanyi ne Kina iya qara nono mai dan tsami cikin qullun ki, sannan ki sake rufe shi ki mayar wurin mai dumi zuwa awa daya saiki dauko zaki ga ya tashi sosai.

  3. 3

    Zaki yanka albasa ki juye sugar dinki ki sake mixing sannan zaki dandana qullun ki in yayi tsami Kina iya saka kanwa in bayyi tsami ba Bakya buqatar kanwa,Zaki dora tanda na suya Waina in ki kan wuta kisa wuta daidai saiki na saka mai kamar 2spoons ki debo qullun kamar ludayi 1 da rabi, a hankali in ta soyu ki juya bayan in yayi kisa cokali ki fitar da ita hankali haka xa kiyi sauran har ki gama.

Reactions

Edit recipe
See report
Share

Comments

Written by

Ayyush_hadejia
Ayyush_hadejia @cook_14256791
on
Jigawa State Nigeria

Similar Recipes