Edit recipe
See report
Share
Share

Cooking Instructions

  1. 1

    Da farko dai zaki daka/niqa kayan miyanki(tumatir,tarugu da tattasai),sanna ki yanka albasan ki a wani kwanon da ban ki ajiye su a gefe.

  2. 2

    Saiki wanke carrot dinki ki yanka shi daban Shima,daganan ki wanke green beans dinki Shima ki ajiye gefe,sannan ki yanka cabbage dinki.

  3. 3

    Sai ki dora tukunya akan murhu/stove,ki soya manki da albasa idan ya soyu sai ki zuba kayan miyanki.

  4. 4

    Dazaran kayan miyanki sun fara tafasa sai ki zuba green beans dinki don ya dahu sosai

  5. 5

    Sannan sai ki dauko hantar ki,ki gayara ta sosai sai ki tafasa ta da albasa da citta kadan saboda qarni.

  6. 6

    Bayannan sai ki sauke hantan ki yanka shi kanana kanana,sai ki zuba cikin kayan miyanki dake kan wuta.

  7. 7

    Idan ta Kusa dahuwa sai ki zuba albasan ki da carrot dinki.

  8. 8

    Sannan ki dauku su maggin ki da su curry ki zuba.

  9. 9

    Idan ta soyu sai ki zuba cabbage dinki ki barshi ya dahu.

  10. 10

    Idan ta dahu/soyu,saiki dafa shinkafa ki hada da miyar aci.

Edit recipe
See report
Share
Cook Today
Mrs Ishaq Alheri
Mrs Ishaq Alheri @cook_16212873
on
Kaduna State
I really love to cook, cooking is my hobby
Read more

Comments (5)

Ummu Irfan's Kichten
Ummu Irfan's Kichten @HAFSATKHALEED6
Amma green beans din xai dahu acikin miyar?basai kadafashi daban ba sannna kaxuba?

Similar Recipes