Miyar yakuwa zalla da danyen kifi

Jantullu'sbakery
Jantullu'sbakery @jantulluhadiza84
Sokoto

Wannan miyar a garin mu Argungu(jahar kebbi)itace miyan da akafi so, dalili kuwa akwai kifi sosai a garin haka ma yakuwan.kuma ita wannan miyan anfi cinta da tuwon jar shinkafa(Gadon gida)

Miyar yakuwa zalla da danyen kifi

Wannan miyar a garin mu Argungu(jahar kebbi)itace miyan da akafi so, dalili kuwa akwai kifi sosai a garin haka ma yakuwan.kuma ita wannan miyan anfi cinta da tuwon jar shinkafa(Gadon gida)

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Dafarko zaaji jajjagen kayan miya, a dora tukunya awuta a zuba manja da albasa a zuba jajjagen a soya sosai

  2. 2

    Bayan jajjagen ya soyo zaa zuba ruwa (mai dan dama)a zuba su maggi da gishi, zaa zuba kayan kanshi da daddawan da aka daka

  3. 3

    Bayan an saka komi zaa zuba danyen kifin arufe tukunya, abar miyan yayi ta dahuwa.

  4. 4

    Idan miyan ya dade yana dahuwa, zaa bude aga idan ruwan miyan ya kai yadda ake son yawan miyan

  5. 5

    A wannan lokacin zaa cire kifin dake cikin miyan ajiye gefe, zaa zuba kulin da aka daka acikin miyan, anan kuma zaa zuba yakuwan da ka wanke aka gyara hade da ganyen albasa se a rufe miyar

  6. 6

    Bayan kaman 15munites haka zaa bude tukunyan a asa whisker ayi whisking sosai da sosai, anan zaa mayar da kifin a miya a juya sannan rage wuta sosai(idan kina so zakiyi whisking kifin a miyan, amman wajen dakeda yara is not advisable ayi hakan din)

  7. 7

    Bayan mintuna ukku zuwa hudu zaa ga mai ya taso saman tukunya, miyar yayi kenan a saukar.

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Jantullu'sbakery
Jantullu'sbakery @jantulluhadiza84
rannar
Sokoto
I love cooking,i love been creative and I love sharing my recipies 💓❣️💃
Kara karantawa

sharhai (5)

khadija (Deejarh bakery)
khadija (Deejarh bakery) @khadija02
Kai inason miyar yakuwa wlh kamn ki aikomun

Similar Recipes