Masa/waina

Masu dafa abinci 4 suna shirin yin wannan
Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Shinkafan tuwo kofi hudu
  2. Shinkafa dafaffa rabin kofi
  3. Yeast cokali daya
  4. Kanwa kadan
  5. Kwai daya
  6. Sugar
  7. Gishiri kadan
  8. Fulawa
  9. Mai

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Zaki wanke shinkafan tuwo ki barshi na tsawon mintuna sai ki markada ta gari.

  2. 2

    Zaki tankade garinki kisa masa dafaffan shinkafa da kika tuka kamar zakiyi tuwo,kisa fulawa, kanwa,sugar da gishiri ki kwaba shi ruwa ruwa dai dai kullin waina ki ajiye ki barshi ya kwana.

  3. 3

    Ana saura awa biyu da suya kisa yeast.Bayan ya tashi kafin suya kisa kwai da albasa ki motsa.

  4. 4

    Ki dora tanda ki zuba mai idan yayi zafi ki debo kullin ki zuba idan dayan gefen ya soyu sai ki juya(karki cika wuta kuma karkisa kullin da yawa gurin suya).

  5. 5

    Idan yayi sai a kwashe a sa a flask.Aci da miyan da ake so.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
fauxer
fauxer @fauxer
rannar
kebbi State
many listen to music when depressed . When in such situation i go to my kitchen. Cooking is the only thing that can never get me exhausted and makes me forget my worries
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes