Masa da miya

Ayshat Adamawa(U. Maduwa)
Ayshat Adamawa(U. Maduwa) @Ayshat_Maduwa65
Abuja

Masa Masa Masa tun banason Masa har na Fara sonshi Dan shine favorite breakfast na oga, tun inayin baya kyau har na Zama gwana gunyin Masa alhamdulillah. Karla taba give up a rayuwa,. Idan har Zan iya Masa tayi Kya haka toh Ina Mai tabbatar muku ba wadda bazai iyayin ba.

Masa da miya

Masa Masa Masa tun banason Masa har na Fara sonshi Dan shine favorite breakfast na oga, tun inayin baya kyau har na Zama gwana gunyin Masa alhamdulillah. Karla taba give up a rayuwa,. Idan har Zan iya Masa tayi Kya haka toh Ina Mai tabbatar muku ba wadda bazai iyayin ba.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

awa daya
mutane hudu
  1. Shinkafan Tuwo cup 3
  2. cupDaffafen shinkafan Rabin
  3. Yeast chokali babba biyu
  4. Albasa karami gida daya
  5. Citta danye kadan
  6. Sugar yadda ake bukata
  7. Gishiri kadan
  8. Baking powder kadan
  9. Mai soyawa
  10. Miya ko yaji ko zuma

Umarnin dafa abinci

awa daya
  1. 1

    Da farka Zaki jika shinkafar ki danye. Amma Ni gaskiya bana dogon jikawa wani lokaci ma idan na tashi sallan asuba Zan jika Nan da awa daya sai na nika Kuma lfy Lau👌

  2. 2

    Sai ki wanke ki zuba ahinkafan a robaki hada daffafiyar da danyen da citta sai Kuma Dan albasa.

  3. 3

    Sai ki Kai a nika idan Kuma blendan ki na da karfi saiki nika dashi. Idan a gida Zan nika Ina hadawa da yeast Amma idan zankai engine gaskiya bana sawa.

  4. 4

    Sai ki ajiye a guri Mai duni ya tashi na Dan wani lokaci

  5. 5

    Idan ya tashi saiki Dan yanka wani albasa kadan kisa, sai kisa gishiri,sugar da Dan baking powder idan ana bukata. Sai ki Kara mishi ruwa Dan ba ason yay tauri

  6. 6

    Sai ki tanadi tandarki ki zuba Mai aciki ki Fara soyawa har sai yayi Miki yadda kikeson

  7. 7

    Sai kici da miyanda kikeson ko Zuma ko sugar ko yaji duk wadda yayi Miki.

  8. 8

    Aci Dadi lfy

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Ayshat Adamawa(U. Maduwa)
Ayshat Adamawa(U. Maduwa) @Ayshat_Maduwa65
rannar
Abuja
cooking is my dream and also cooking is all about being creative
Kara karantawa

Similar Recipes