Brodi mai kirfa(cinnamon bread)

TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA)
TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA) @cook_15480513
Port Harcourt

Yarana sunason brodi sosai shiyasa nake yawan yimusu ta hanyan sarrafashi tafanni daban daban. Kuma wannan brodin yanada dadi sosai#BAKEBREAD

Brodi mai kirfa(cinnamon bread)

Mai dafa abinci 1 yana shirin yin wannan

Yarana sunason brodi sosai shiyasa nake yawan yimusu ta hanyan sarrafashi tafanni daban daban. Kuma wannan brodin yanada dadi sosai#BAKEBREAD

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Fulawa kofi uku
  2. Zuma rabin kofi
  3. Yeast chokali daya
  4. Baking powder half tea spoon
  5. Kwai daya
  6. Flabo chokali daya
  7. Garin kirfa chokali biyu
  8. Butter chokali biyu
  9. Ruwa rabin kofi

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Zakisamo bowl mai tsapta ko roba sai kizuba ruwa aciki sannan kixuba zuma da yeast tareda baking powder da kwai da butter sai ki kadasu da kyau harsawon minti uku said kizuba fulawarki day kunriga da kintankade sai ki kwabaci da kyau har sawon minti biyar sai kirufeshi kibarshi zuwa minti goma don yatashi

  2. 2

    Bayan yatashi sai kidaukoshi kimaidashi inda zakimurza sai kidan barbada fulawa awurin dakuma kan dough din sai kimurzata day kyau sai kirabashi gida biyu sannan kidauko abun gasa brodin sai kishafa butter aciki sannan kikoma kan dough din. Sai kidau kashi dayan kisake rabashi gida biyu sai kimurzashi yayi dogo sai kihada bakinsu su biyun sai kiringa nannadesu. Haka zakiyiwa dayan ma

  3. 3

    Bayan kingama murzawa sai kihada bakin su biyudin sai kiringa nannadeshi kamar haka sannan kisashi cikin pan din bayan kingama sai kirufeta ki ajiye zuwa awa days sai ki kunnaoven don kigasashi. Bayan kingasa sai kibarshi yahuce sann an kisaka aleda don takaralaushi

  4. 4

    Shikenan nagama aci dadi lfy

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA)
rannar
Port Harcourt
Gskiya arayuwata inason girki sosai shiyasa kullum ina kicin wurin tsara abinci kalakala
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes