Fanke mai cakulet

Afaafy's Kitchen
Afaafy's Kitchen @mohana10
Kano

Na kasance safiyar yau ina sha'awar cin fanke,na tafi madafa domin hadawa sai nace mai zai hana in dan fito da wani samfuri😂😂....naji dadin wnn fanken.

Fanke mai cakulet

Masu dafa abinci 2 suna shirin yin wannan

Na kasance safiyar yau ina sha'awar cin fanke,na tafi madafa domin hadawa sai nace mai zai hana in dan fito da wani samfuri😂😂....naji dadin wnn fanken.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Fulawa
  2. Garin cocoa
  3. Sukari
  4. Mai
  5. Madara (ta ruwa ko majinar bature😂)
  6. Yeast
  7. Baking powder

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Ki jiqa yeast da ruwa mai dumi a cikin dan kwano ko kofi mai kyau ki ajiyeshi yy kmr minti 10

  2. 2

    Ki tankade fulawa da garin cocoa cikin roba mai dan fadi,ki saka sukari (adadin yadda kike son zaqin ya kasance)

  3. 3

    Ki saka baking powder,ki diga mai kadan ki cakude shi

  4. 4

    Ki zuba madara da jiqaqqen yeast dinki ki cakedeshi ki buga sosai,ki rufe ki barshi ya tashi.

  5. 5

    Ki dora mai a wuta,in yy zafi ki riqa diba kina soyawa🤗......aci dadi lpy.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Afaafy's Kitchen
rannar
Kano

sharhai

Similar Recipes