Faten doya

Masu dafa abinci 2 suna shirin yin wannan
Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Doya
  2. Tafashen nama
  3. Crayfish
  4. Jajjagen kayan miya
  5. Albasa
  6. Manja
  7. Chitta da tafarnuwa dakakke
  8. Kayan kanshi
  9. Dandano
  10. Gishiri
  11. Ruwa

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko ki yanka doyanki kanana dai dai yin fate sai ki wanke ki aje gefe.ki dora tukunya kan wuta sai ki zuba manja ki yanka albasa ki zuba kadan ki aje sauran.sai ki zuba chitta da tafarnuwa ki juya ki barshi ya dan soyu.

  2. 2

    Idan ya soyu sai ki kawo kayan miyan ki ki zuba ki soya sama sama sai ki zuba namanki da ruwan tafashen, ki zuba dandano,kayan kanshi, crayfish, dan gishiri sai ki zuba ruwa dai dai sannan ki kawo doyar ki zuba ki juya sai ki rufe.

  3. 3

    Idan ya kusa nuna sai ki zuba sauran albasan ki kara ruwa idan da bukata ki rufe ki rage wuta ya karasa.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
mhhadejia
mhhadejia @mhhadejia1975
rannar
Kaduna State, Nigeria

sharhai

Similar Recipes