Sandwich (Biredi mai hadi)

Mai dafa abinci 1 yana shirin yin wannan
Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

20mintuna
3 yawan abinchi
  1. Biredi mai yanka guda 12
  2. Kifi sadin gwangwani 1
  3. Mayonis cokali cin abinci 4
  4. 1Rabin maggi guda
  5. 3Tumatir guda
  6. Cucumber 1 karami
  7. Wayan lettuce yanda kike da bukata
  8. Albasa rabi
  9. 4Dafaffen kwai
  10. Dakakken masoro kadan

Umarnin dafa abinci

20mintuna
  1. 1

    Da farko zaki fara dako biredi ki jera kaman guda hudu sai kisa wukar yanka biredi ki yanke gefe da gefen.Sai ki aje su a leda kada ya bushe.

  2. 2

    Ki sami kwano mai kyau ki bude gwangwanin sadin ki tsiyayye man a wani mazu,ki juye kifin a kwano ki bareshi ki cire kaya da zaren.Sai kisa cokali mai yatsu ki marmasa kifin sannan a dako dafaffen kwai a bare a yankashi matsakaita a hadesu da kifin a zuba mayonis a juya.

  3. 3

    Sai a zuba maggi kadan,albasa,masoro kadan,a kara mayonis sai a juya.Ki dako biredin ki guda daya ki zuba masa wannan hadin kifin sai ki aje ki dako wani biredin ki jera letuce,cucumber da tumatir bayan kin yankasu rawun,sai ki dora akan daya biredin mai hadin kifi,ki kawo wani mai hadin kifin ki dora akai.Sai ki rufe ki yanka da wuka iya shape da kike so. #tnxsuad

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Bint Ahmad
Bint Ahmad @Bint92
rannar
Sallari,Kano Nigeria.
For me,the kitchen is the most special room in the house.Its a place for adventure -not drudgrey,but discovery,sharing and showing off with friend's,trying new ideas.♡☆
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes