Sandwich a saukake

Khady Dharuna
Khady Dharuna @antynanah2022
Kano, Meduguri Road, Tarauni.

Girkin yanada dadi sosai ga kara lfy gashi baida nauyi ya hada kayan marmari, mukan ci shi yayin sahur hade da ruwan dumi me lemon da sugar. Yana taimakawa ya rike ciki. #sahurrecipecontest

Sandwich a saukake

Masu dafa abinci 10 suna shirin yin wannan

Girkin yanada dadi sosai ga kara lfy gashi baida nauyi ya hada kayan marmari, mukan ci shi yayin sahur hade da ruwan dumi me lemon da sugar. Yana taimakawa ya rike ciki. #sahurrecipecontest

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

minti 30mintuna
mutane da yawa
  1. Bread me yanka yanka
  2. 5Karas manya guda
  3. 2Cucumber manya guda
  4. 5Tumatir masu kyau guda
  5. 1Albasa Babba guda
  6. 7Dafaffen kwai guda
  7. Nikakken nama Rabin kilo
  8. Magi domin dandano
  9. Jajjagen tarugu da albasa cokali 1
  10. Curry
  11. Spices
  12. Mai cokali 2

Umarnin dafa abinci

minti 30mintuna
  1. 1

    Ga kayayyakin da za ayi amfani da su nan.

  2. 2

    A wanke nikakken nama a tsane a kwalanda sannan a Dora shi akan wuta. Saka maggi, kori, kayan kamshi da albasa a zuba ruwa barshi ya dahu har ruwan ya kafe a jikinsa sai a sauke

  3. 3

    A wanke Kara's a kankare bayan sai a yanyankashi a kwance, sannan a wanke tumatir da cucumber a yayyanka su a kwance. A yayyanka dafaffen kwai ma a kwance.

  4. 4

    A Dora kasko akan wuta a zuba mai kadan sannan a saka yankakkiyar albasa da Dan yawa a juya, Idan ya fara soyuwa sai a saka attaruhu da albasa a juya na minti 5 sai a zuba Kara's shima na minti 5 a juya sai a kawo nikakken nama da aka dafa a zuba a kara spices sai a barshi mintuna 2 a sauke.

  5. 5

    A dauko fallen bread a zuba hadin naman akai

  6. 6

    Sannan a saka tumatir, cucunber da kwai.

  7. 7

    Daganan sai a kara zuba hadin naman akai a rufe da daya fallan bread din.

  8. 8

    Sannan sai ake sakawa a manual toaster a gasa. Idan gefe yayi sai a juya gefe ma.

  9. 9

    Idan ya gasu sai a cire. Acishi da duminsa yafi dadi

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Khady Dharuna
Khady Dharuna @antynanah2022
rannar
Kano, Meduguri Road, Tarauni.
cooking is my dream!!!
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes