Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Ganyen lafsir
  2. Tumatur
  3. Albasa
  4. Dakakken quliqul
  5. Kayan qamshi
  6. Kayan dandano
  7. Jan yaji
  8. Cucumber

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    A wanke ganyen sosai sai a yanka, sai a zuba gishiri a ruwa asaka yan kakken ganyen a ciki abarshi kamar minti 15-20, sai a tsame a sa a gwagwa a barshi ya tsane.

  2. 2

    Sai a wanke cucumber, tumatur da albasa a yankasu yanda ake buqata a ajiyesu gefe guda.

  3. 3

    Asamu roba mai tsafta a zuba quliquli, kayan qamshi, yaji da kayan dandano sai a zuba ruwa a kwa6asu gaba daya, sai a zuba lafsir din dasu tumatur din gaba daya a cakudasu shikenan sai a rabawa jama'ar gida.

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Hauwa Dakata
Hauwa Dakata @hauwa1993
rannar
Kano

sharhai

Similar Recipes