Kunun gyada

Ummu ashraf kitchen
Ummu ashraf kitchen @cook_19629121
Kano

#FPPC Ramadan kareem😍😍

Kunun gyada

sharhuna da aka bayar 3

#FPPC Ramadan kareem😍😍

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

30mins
5 yawan abinchi
  1. Danyar gyada kofi biyu
  2. Dafaffiyar shinkafa rabin kofi
  3. Sugar rabin kofi (idan kina san sugar dayawa sai ki kara)
  4. Madara babban cokali biyar
  5. Leman tsami daya
  6. Filawa kofi daya

Umarnin dafa abinci

30mins
  1. 1

    Da farko zaki gyara gyadar ki,ki wanke ta,ki shanyata ta bushe sai ki soyata sama sama ki murje ta bawan ya fita,sai a kai markade, idan an markado miki ki tace da abin tata ko rariya,sai ki zuba a tukunya ki dura a wuta ki dakko dafaffiyar shinkafar ki ki zuba a ciki kina juyawa har ya tafasa(yayin da kika dura kullin a wuta baza ki tashi ba saboda kar ya tafaso ya zuba, sai kina zaune a gurin kina juyawa) sai ki dakko filawarki ki damata da ruwa ya danyi kauri.

  2. 2

    Idan ya tafasa sai ki zuba damammiyar filawarki a ciki a hankali kina juyawa har kaurinsa yayi miki yadda kikeso sai ki sauke ki matsa leman tsami a ciki ki juya,

  3. 3

    Ki barshi ya huce sai kisa sugar da madara asha😋(shi sugar din sai kunun ya huce ake zubawa saboda in kika zuba sugar da zafi shine yake sa kunun ya tsinke).

  4. 4

    Done......😍😍

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Ummu ashraf kitchen
Ummu ashraf kitchen @cook_19629121
rannar
Kano
I luv cooking
Kara karantawa

Similar Recipes