Tuwan shinkafa miyan Kuka da manshanu

Mamu
Mamu @1981m
Lagos
Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

mutum biyu
  1. Kofi 2 na shinkafa
  2. Ruwan dazai dafata
  3. Miyar kuka
  4. Kuka
  5. Daddawa
  6. Jajjagen albasa, attarugu/ tatasai
  7. Manja
  8. Sinadaran dandano
  9. Nama/kifi

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Nasa ruwan zafi a wuta nabarshi harya tafasa, nawanke shinkafar tuwo nazuba aciki, nabarshi harya dahu, daya dahu na dauko muciya natuka sosai har yayi taushi, sannan nakara zuba ruwa kadan narufe shinkafar harya sulala, dayayi nakara saukewa natuka, nakawo ledar turo na kulla aciki.

  2. 2

    Natafasa nama a wuta daya dahu nakwashe, sanan na xuba manja nakawo jajjagen kayan miya naxuba aciki, nakawo daddawa naxuba aciki, naci gaba da soyawa, sannan naxuba naman aciki da sinadaram dandanano, nakawo ruwan nama nasa aciki, nabarshi yayita dahuwa, da ruwan miyar yayi mani yadda nakeso, saina kawo kuka ina xubawa ina kadawa har daidai kaurin danakeso, saina barshi, yadan dahu kadan saina kawashe.

  3. 3

    Anaci da manshanu don akwai dadi sosai.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Mamu
Mamu @1981m
rannar
Lagos
Eating is necessity but cooking is an Art, i just love cooking
Kara karantawa

Similar Recipes