Tuwon shinkafa da miyar kuka

Mrs,jikan yari kitchen
Mrs,jikan yari kitchen @mrsjikanyari

#gargajiya wannan tuwon yaseen naci kusan leda biyu gsky abincinmu na gargajiya da daɗi karmu yada

Tuwon shinkafa da miyar kuka

#gargajiya wannan tuwon yaseen naci kusan leda biyu gsky abincinmu na gargajiya da daɗi karmu yada

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Shinkafa
  2. Ruwa
  3. Leda
  4. Tattasai
  5. Attarugu
  6. Nama/kaza
  7. Daddawa
  8. Baƙin yaji
  9. Cittah
  10. Tafarnuwa
  11. Maggi
  12. Mai
  13. Albasa
  14. Garin miyar kuka

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko xaki ɗora tukunyarki ki xuba ruwa dai dai wanda xai dafa maki tuwonki idan ruwan yafara xafi saiki wanke shinkafarki ki xuba kibata 45 or 1hr xakiga wani kumfa yafara tasowa idan yabushe kamar ƙanxo yadahu kenan saiki sauke kisaka abun mulƙawa mucciyya ki mulƙa sosai xayyi kamar flour saiki kwashe kirinƙa sakawa a leda fara or baƙa shikenan kin gama tuwon shinkafarki

  2. 2

    Da farko miyar kuka xaki fara wanke kayan miyarki ki jajjaga or blending kiɗora ki xuba mai kisaka albasa idan tafara soyuwa saiki xuba kayan miyarki miyar gargajiya tana buƙatar saita soyu sosai sannan ki xuba ruwa shixai saka komai yayi xam xam kisaka kayan yajinki da maggi da namanki/kaxa kisaka har ruwan tafasar kibata 30mnts hmmm sannan kiɗauko garin kukarki kisaka mixer kina xuba miyar kina burkakawa shikenan kibata 5scnd saiki sauke uhmm daɗi sai wanda ya gwada xai bani bayani🤤😋

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Mrs,jikan yari kitchen
rannar

sharhai (24)

Mrs Mubarak
Mrs Mubarak @maanees_kitchen
Woow gaskiya yayimin kyau ko afuska da akwai sauran dumame abani inci 😋😋

Similar Recipes