Kayan aiki

  1. Nama
  2. Kwai 3
  3. Dandano
  4. Kabeji 1
  5. Albasa 1
  6. Kanunfari
  7. Mai
  8. Attaruhu 5

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko zaki yanka nama madai-daita saiki dorashi a tukunya ya dahu kisa gishiri da kayan kamshi kibari ya dahu yayi liguf,sannan saiki yanka kabeji ki ajje a gefe

  2. 2

    Idan yayi liguf saiki sauke kibari yasha sannan ki dakashi kamar zakiyi dambun nama amman kada yayi laushi kamar na dambun naman idan ya daku

  3. 3

    Saiki kwashe shi,saiki jajjaga attaruhu sannan ki dakko kwai ki fasa shi a kwano saiki zuba dan dano da kayan kamshi da kabeji da attaruhun da kika jajja ki juyasu sannan

  4. 4

    Saiki dakkon dakakken namanki ki zuba aciki ki jujjuya

  5. 5

    Sannan saiki dakko kaskon suyar waina/masa ki dora a wuta idan yayi zafi saiki zuba ki rinka debo wannan naman kina zuwa aciki kada ki cika wuta saboda asamu ya soyu idan yayi sae ki juya

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Zully_skitchen
Zully_skitchen @Z08123005896
rannar
gaida falwaya me dakali

Similar Recipes