100pcs Cupcake

Sam's Kitchen
Sam's Kitchen @Sams_Kitchen
Yobe State

Recipe din nan yana da dadi sosai ga auki sannan kuma ga laushi zakiyi amfani dashi sbd event, biki, suna, sallah da dai sauran su

#method
#skg

100pcs Cupcake

Recipe din nan yana da dadi sosai ga auki sannan kuma ga laushi zakiyi amfani dashi sbd event, biki, suna, sallah da dai sauran su

#method
#skg

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. 9 cupsflour
  2. 3Butter
  3. 3 cupsSugar
  4. 20Kwai
  5. 3 tbB powder
  6. 1 cupButtermilk
  7. 3drop of vanillah

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Zaki zuba butter dinki a cikin bowl mai fadi saiki zuba sugar kisa mixer ko whisker ko muciya ki buga su sosai da sosai har sai butter dinki tayi laushi sosai kuma tayi haske sosai (Idan da whisker ko muciya zakiyi zai kai tsawon 25 to 30mnts kina bugawa idan kuma da handmixer ne zai dauki tsawon 15mnts)

  2. 2

    Zaki fasa kwai dinki da bibbiyu kina sawa kina bugawa har ki gama, (karfa kisa kwai dinki lokaci daya)

  3. 3

    Saiki hada flour da baking powder ki zuba a hankali shima ba lokaci daya zaki saka ba har sai flour dinki y kare ki juya sosia komai y hade normal

  4. 4

    Saiki saka drop na vanillah da kuma butter milk ki juya sosai komai ya hade shknn kin gama hadin cupcake dinki

  5. 5

    Zakiyi preheating oven kisa papers a pan ki zuba hadinki saiki gasa tsawon 15mntsi da wutar kasa kawai (amma fa ya danganta da yanayin zafin oven dinki), bayan wannan lokacin zaki bude ki rage wutar sama ki kaita can kasa saiki kunna ta sama kisata itama can kasa zuwa 5mnts shknn kin gama baking

  6. 6

    Ayi hidima lafiya 😃

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Sam's Kitchen
Sam's Kitchen @Sams_Kitchen
rannar
Yobe State
Cooking is my favorite
Kara karantawa

Similar Recipes