Tura

Kayan aiki

10 yawan abinch
  1. Barzaza shinkafa
  2. Zogala
  3. Tattasai da tarugu
  4. tafarnuwaAlbasa da
  5. Geda nikakka
  6. Mai da Magi ajino moto
  7. Maggi star da gishiri
  8. Ruwa

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko xaki wanke barzaza shinkafarki seki batta da yan ruwa yadda xata jika kafin ki gama dahuwar zogalarki da jajjagen kayan miya

  2. 2

    Seki gyara zogalarki ki wanketa ki azata saman murhu kisa mata sugar kadan da tsamiya yadda zatayi Zaki

  3. 3

    See kiyi jajjagen tattasai da tarugu d albasa d tafarnuwa inkin gama seki xuba kayanki waje guda hadda gedarki takakka kamar haka

  4. 4

    Kisa Mai da Magi ajino moto da star da gishiri duk kisa ciki seki juyashi sosai kamar haka

  5. 5

    Seki aza tukunyarki kan wuta kisa ruwa ciki sannan kisama gwagwaki mai kafin kisata cikin tukunya inkin xuba danbum cikin gwagwa ki samu buhu mai tsafta ko leda ki kulle danbum da Shi yadda suraci xe bugi danbum dakyau

  6. 6

    Bayan minti goma sha biyar kina iya budawa ki duba in danbunki na bukatar ruwa sekimai yayyafi ki kulle shi in yayi xakiji kamshi na tashi shikenan seki sauke aci dadi lfy😋

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Asma'u Muhammad
rannar

Similar Recipes