Kayan aiki

  1. Shinkafa
  2. Man gyada
  3. Alayyahu da albasa mai lawashi
  4. Tarugu da tatasai
  5. Magi ajino moto
  6. Magi star
  7. Curry da mixpy
  8. Ruwa
  9. Gishiri

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko xaki gyara shinkafarki ki kaita wurin nika amiki barxo

  2. 2

    Saeki wanki barxonki kisa magi ajino moto da gishiri da curry ciki sae ki axa tukunya saman murhu kisa gwagwa ciki saeki xuba barxon shinkafarki ciki ki bashi yayii minti arba'in saiki jissuwa ki xubi cikin kwana babba yadda xakiji dadin hawashi Kamar haka

  3. 3

    Saeki jajjaga tattasai da tarugu da albasa ki aje gihe saeki xo ki yanka alayyahun ki da albasa mai lawashi

  4. 4

    Seaki xuba jajjagenki da yankakin alayyahunki da albasa da Maggi ajino moto da gishiri da Maggi Star da mixpy da ruwa kadan da Mai duk cikin barxon shinkafarki da kinka turara seki juyashi harsu hade wuri guda Kamar haka

  5. 5

    Saeki maidashi cikin tukunya ki kulle ki bashi minti talatin xuwa arba'in zakiji ya fara kamshi seki jissuwa

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Asma'u Muhammad
rannar

Similar Recipes