Tuwon shinkafa da miyar ganye

Euphoria’s spot
Euphoria’s spot @euphorias_spot01

Tuwon shinkafa da miyar ganye

Masu dafa abinci 19 suna shirin yin wannan
Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

1 hr 30 minutes
6 people

Umarnin dafa abinci

1 hr 30 minutes
  1. 1

    Ki wanke shinkafar tuwonki ki zuba ruwa sai ki dorata a wuta under low heat ki rufe ki rabu da ita har sai tafara radaddagewa da kanta kuma ruwan ya shanye

  2. 2

    Sai ki tuka tuwonki a wurin tukawar sai ki zuba semo ki tuka idan ya tuku, Sai ki saka ruwa kadan ki kara rufewa for some minutes sai ki kara tukawa ki kwashe a leda

  3. 3

    Sai ki wanke tattasai, tarugu, tumatur da albasa kiyi blending dinsu, sai ki dura tukunyarki a wuta ki saka vegetable oil dinki yayi zafi sai ki zuba kayan miyarki sai ruwan ya tsotse sukuma sun soyu

  4. 4

    Kina jiransu sai ki wanke kabeawarki ki fereta ki dafata sai ki markada ki zuba a cikin miyarki sai ki dauko agushinki shima ki zuba

  5. 5

    Sai ki wanke Allayyahuki ki yanka shima ki zuba cikin miyarki sai ki daka crayfish dinki ki zuba sai ki kawo seasonings dinki suma ki zuba sai ki jira miyarki ta ida

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Euphoria’s spot
Euphoria’s spot @euphorias_spot01
rannar

sharhai

Similar Recipes