Dafaffan doya da jan miya da kifi

Mai dafa abinci 1 yana shirin yin wannan
Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. doya karami guda daya,
  2. ,tumatir guda goma
  3. ,tarugu guda uku l
  4. tattasai guda biyu
  5. Albasa guda daya,
  6. magi ,guda hudu
  7. manja rabin kofi
  8. kayan kamshi rabin cokali
  9. kifi yanda kike so
  10. gishiri kadan

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko zaki fere doya ki yanka kanana sai ki wanke kisa akan wuta ya dahu Inyayi kisa a kolanda ruwan ya tsane

  2. 2

    Zaki wanke tumatir,tarugu,tattasai da albasa ki nika sai kisa acikin tukunya ki daura akan wuta,zaki barshi ruwan ya shanye sai kisa manja aciki ki soya kayan miyan inya soyu sai kisa ruwa aciki

  3. 3

    Inya tausa sai kisa magi da kayan kamshi,zaki wanke kifi kisa gishiri sai ki soya inya soyu ki zuba acikin miyan,idan miyan yayi sai kisa a filat aci lfy

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Amina Aminu
Amina Aminu @cook_13830126
rannar
zaria,kaduna state

sharhai

Similar Recipes