Garau garau

Amcee's Kitchen
Amcee's Kitchen @Amina69
Zaria,kaduna State

Garau garau abinci ne da yayi suna musamman arewacin kasannan, ana yin garau garau ta hanyan shinkafa,wake da gishiri, amma yanzu da zamani yazo ana kara masa kayan lambu kaman su latas,latas,kokumba da dai sauransu..kuma abinci ne me kara lafiya balle wake yanzu zan nuna maku yanda nake garau garau dina#garaugaraucontest

Garau garau

Garau garau abinci ne da yayi suna musamman arewacin kasannan, ana yin garau garau ta hanyan shinkafa,wake da gishiri, amma yanzu da zamani yazo ana kara masa kayan lambu kaman su latas,latas,kokumba da dai sauransu..kuma abinci ne me kara lafiya balle wake yanzu zan nuna maku yanda nake garau garau dina#garaugaraucontest

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Shinkafa Kofi biyu
  2. Wake Kofi daya
  3. Gishiri dan kadan
  4. Magi guda biyu
  5. Man gyada kwatan Kofi
  6. Latas falls goma
  7. Koran tattasai guda daya
  8. Timatir guda uku
  9. Albasa guda daya
  10. Karas guda biyu
  11. Kokumba rabi
  12. Yaji yanda kike so

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Zake gyara wake ki wanke sai kisa acikin tukunya da ruwa kisa akan wuta kar ki ciki wuta saboda inyayi yawa zaki ta kara ruwa kuma bai nuna ba anaso abarshi ya nuna sosai,idan yayi said ki sauke ki kisa ruwa aciki ki samu kolanda ki tsane ruwan said kisa a gefe

  2. 2

    Zaki sa shinkafa a roba kisa gishiri sai ki wanke kisa a tukunya kisa ruwa ki daura akan wuta yadan tafasa na minti biyu,idan yayi sai ki sauke ki kara daura yewa ki mai da kan wuta ya kara nuna idan yayi sai ki sauke

  3. 3

    Zaki wanke latas da gishiri ki yanka kanana,ki wanke timatir ki yanka kanana,ki wanke Koran tattasai ki yanka kanana

  4. 4

    Sai ki yanka albasa ki yanka kanana,ki wanke kokumba ki yanka kanana

  5. 5

    Zaki kan kare bayan karas ki yanka kanana sai kisamu filat ki jera su kaman haka

  6. 6

    Sai kisa shinkafa da wake filet kisa yaji,magi da man gyada aci garau garau lafiya

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Amcee's Kitchen
rannar
Zaria,kaduna State
cooking is my fav
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes