Kosan doya

Afrah's kitchen
Afrah's kitchen @Afrah123
Kano

Kosan doya na daya daga cikin abincin karyawa da safe da shayi ko kunu. Ga dadi Ga saurin yinshi.

Kosan doya

Masu dafa abinci 3 suna shirin yin wannan

Kosan doya na daya daga cikin abincin karyawa da safe da shayi ko kunu. Ga dadi Ga saurin yinshi.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

2 yawan abinchi
  1. Doya karama
  2. 2Kwai
  3. Attaruhu 3 manya
  4. 1Albasa
  5. 2Maggi
  6. Onga cokali daya karami
  7. Mai cokali 3
  8. Gishiri cokali 1 karami
  9. Sukari cokali 1 karami
  10. Curry cokali 1 karami
  11. Flour cokali 2
  12. Mai na suya

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Zaki fere doyarki kiwanketa ki yanka ta kanana kisa atukunya da ruwa da gishiri da sukari ki dafata yayi laushi.

  2. 2

    Ki jajjaga attaruhu da albasa kisa mai a kasko ki soya kisa maggi,curry su soyu ki sauke.

  3. 3

    Ki juye doyar da kika dafa a roba me dan zurfi ki marmasa ta ko ki daketa sannan ki juye soyayyen jajjagen da kikayi ki cakuda sosae.

  4. 4

    Ki rika diba kina mulmulashi yayi kamar ball har ki gama sannan ki barbadeshi da flour sannan ki fasa kwai ki kadashi kisa masa kayan kamshi kawai ki rika tsomawa aciki kina soyawa a mai.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Afrah's kitchen
rannar
Kano
cooking is my fav
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes