Faten tsakin shinkafa me dankalin Hausa

Khady Dharuna
Khady Dharuna @antynanah2022
Kano, Meduguri Road, Tarauni.

Khady Dharuna...girkin yanada dadi sosai musamman sabida kwalama..

Faten tsakin shinkafa me dankalin Hausa

Mai dafa abinci 1 yana shirin yin wannan

Khady Dharuna...girkin yanada dadi sosai musamman sabida kwalama..

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. 1Tsakin shinkafa Kofi
  2. 1Dankalin Hausa madaidaici guda
  3. Kayan dandano
  4. Attaruhu
  5. Albasa
  6. Kayan kamshi
  7. Mai
  8. Nama
  9. Ganyen na'a na'a

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    A wanke nama ya fita sosai, sannan a zuba a tukunya a zuba ruwa a Dora akan wuta, a saka kayan kamshi, gishiri kadan, albasa, magi, hade da kori Idan ya dahuwa sai a ajiye a gefe.

  2. 2

    Dora tukunya akan wuta, zuba mai Dan daidai, yayyanka albasa a ciki Idan yayi zafi soya naman sama sama, Zuba jajjajgaggen attaruhu da albasa a soya na Tsohon minti 5, sannan a zuba ruwan dahuwar naman Idan baida yawa sai a kara da ruwan dumi a rufe.

  3. 3

    Idan ya tafasa sai a zuba kayan dandano, curry, kayan kamshi sannan a kawo tsaki a wanke shi tas a zuba akai a rage wuta, Idan ya rage mintuna kamar 10 zuwa 15 a sauke sai a zuba yayyankakken dankalin Hausa a ciki su karasa dahuwa tare.

  4. 4

    A zuba a faranti sai a tsinki ganyen na'a na'a a sa akai sabida ya bawa girkin abin shaawa.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Khady Dharuna
Khady Dharuna @antynanah2022
rannar
Kano, Meduguri Road, Tarauni.
cooking is my dream!!!
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes