Miyar wake

Khady Dharuna
Khady Dharuna @antynanah2022
Kano, Meduguri Road, Tarauni.

Khady Dharuna. #kanostate.. Miyar tanada dadi sosai.

Miyar wake

Masu dafa abinci 3 suna shirin yin wannan

Khady Dharuna. #kanostate.. Miyar tanada dadi sosai.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Wake gwangwani 3
  2. Kayan miya daidai misali
  3. Albasa
  4. Nama
  5. Kifi
  6. Kayan dandano
  7. Kayan kamshi
  8. Mai
  9. Manja

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    A jika wake Idan ya jiku sai a surfa ko a mitstsike da hannu. A wanke shi a cire dusar a rege tsakuwar sai a ajiye a gefe

  2. 2

    A gyara kayan miya a markada amma albasa tafi yawa, sai a dafasu a ajiye a gefe

  3. 3

    A tafasa nama da kayan kamshi, magi kori da Dan gishiri kadan, kifi a wanke shi da lemon tsami a shanya ya sha iska sannan a soya.

  4. 4

    Sannan a Dora tukunya a zuba mai da manja a sa yar albasa Idan yayi zafi a soya naman sama sama a kwashe, sannan a zuba kayan Miyar a motsa na tsawan mintuna Biyar sai a zuba waken a kara ruwa sosai a juye ruwan naman a ciki a barshi yayi ta dahuwa.

  5. 5

    Idan ya fara laushi sai a zuba kayan kamshi, a juye naman da kifin a saka magi a Dan kara ruwa a motsa sai a rufe a rage wutar ya karasa dahuwa.

  6. 6

    Za a iya ci da tuwo ko shinkafa ko Dan kwadayi a ci da burodi.......

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Khady Dharuna
Khady Dharuna @antynanah2022
rannar
Kano, Meduguri Road, Tarauni.
cooking is my dream!!!
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes