Kosai

Maryam Mukhtar Nayaya ( Mrs A I Zira)
Maryam Mukhtar Nayaya ( Mrs A I Zira) @cook_14450198
Plateau State

Kosai contest by Mrs a i zira

Tura

Kayan aiki

  1. 2 cupsWake
  2. 1Albasa babba
  3. 6Attarugu
  4. 4Tattasai
  5. Man gyada
  6. Ruwa
  7. Tafarnuwa
  8. Gishiri chokali daya

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    A surfa wake a cire dussa

  2. 2

    A gyara albasa, tattasai,attarugu,garlic a sa a wake a marka da su tare.

  3. 3

    In an dawo daka markade sai a sa gishiri, a dauki ludayi ko muciya a buga kullun har sai ya tashi,

  4. 4

    In yayi kauri sai a na kara ruwa.

  5. 5

    Sai a saka man gyada a abun suya asa albasa a huta su soyu.

  6. 6

    Bayan mintuna albasa ta soyu sai ki dauki ludayi kina iban kullun kina sawa a mai.

  7. 7

    Ki bari sai gefe daya yayi ja sai ki juya dayan jefan.

  8. 8

    Sai ki kwashe a matsami ki bari mai ya tsane.

  9. 9

    Inya tsane sai ki sa a plate.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Maryam Mukhtar Nayaya ( Mrs A I Zira)
rannar
Plateau State

sharhai

Jamila Ibrahim Tunau
Jamila Ibrahim Tunau @Jamitunau
@cook_14450198 Duk da cewa anfison kosai lokachin azumi nikam inason kosai 😋😋

Similar Recipes