#KosaiRecipeContest

Rafeeah Zirkarnain
Rafeeah Zirkarnain @cook_13832808
Zaria,kaduna State

Son abu mai gina jiki ya sa ya zama abun Karyawa a gare ni

#KosaiRecipeContest

Masu dafa abinci 4 suna shirin yin wannan

Son abu mai gina jiki ya sa ya zama abun Karyawa a gare ni

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Wake gwangwani biyu
  2. Albasa babba guda
  3. Attarugu kwaya uku
  4. Tattasai biyu
  5. Sinadarin dandano guda biyu
  6. Gishiri gutsure
  7. Man gyadar suya
  8. Dakakkiyar citta Rabin cokalin shayi

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Zaki jiqa waken ki na tsawon Monti biyar,sai ki surfa a Turmi me tsafta don cire dusar waken. Sai ki wanke ta hanyar xuba ruwa cikin waken naki,ki samu matsami kina zubawa dusar na fita har ki tsaftace gaba daya.

  2. 2

    Sai ki wanke attarugun ki,ki wanke tattasai ki cire 'ya'yan ciki,da albasa ki wanke ki raba ta guda shidda sai ki ije kashi guda. Sauran sai ki sa a cikin waken ki.

  3. 3

    Sai ki niqa tai laushi ko a na'urar niqa ta bature ko injin niqa(shi sai ki sa kwano karami da xa a xuba maki ruwar niqar,gudun kar a ci ka maki ruwa). In kin gama sai ki bugata(yana taimakawa gun sa shi a kyau da tashi),in akwai buqatar qarin ruwa sai ki sa ka'dan. Sai ki samu kwano karami ki sa sinadarin dandano,ki sa ruwan xahi cokali uku(hakan zai sa ta narke cikin sauki) sai ki zuba kan kullun waken ki,ki juya ki sa ragowar albasar ki (ki yanka kanana) da cittar ki ki juya ki ije gehe.

  4. 4

    Sai ki sa tsaftataccen paipan suyar ki a wuta,ji xuba mai tai xahi ki dan jefa albasa in yay xahi,sai ki samu chokalin cin abnci ki,kina 'dibar kullun naki kina saka wa cikin mai har ya soyu sai ki kwashe ki sa a abun tsame abu(don mai ya 'di ge.. Ana iya ci da ya ji hakanan ko da koko ko da shayi

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Rafeeah Zirkarnain
Rafeeah Zirkarnain @cook_13832808
rannar
Zaria,kaduna State

sharhai

Similar Recipes