Kosan busashshen wake

teema habeeb
teema habeeb @cook_14150092

Ganin koda yaushe muna amfani da hanya daya tayin kosai shiyasa na gwada nika busassen wake nayi amfani dashi,kuma naji dadinsa sosai nida iyalina kuma sun bukaci da na karayimusu irinshi. #kosairecipecontest

Kosan busashshen wake

Ganin koda yaushe muna amfani da hanya daya tayin kosai shiyasa na gwada nika busassen wake nayi amfani dashi,kuma naji dadinsa sosai nida iyalina kuma sun bukaci da na karayimusu irinshi. #kosairecipecontest

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

Awa daya
2 yawan abinchi
  1. 1kufi daya na kananan wake
  2. 1maggi fari
  3. 1albasa,yankakka
  4. Gishiri kadan
  5. Busasshen shambo
  6. Tafarnuwabiyu
  7. Mai dan soyawa

Umarnin dafa abinci

Awa daya
  1. 1

    Kayanda nayi amfani dasu wurin hada wannan kosai

  2. 2

    Zaki gyara waken da kyau ki cire duk wani datti idan akwai. Sai kisamu blender mai karfi kizuba waken aciki sai ki nikashi sosai

  3. 3

    Bayan kin nikashi sai ki samu matankadi kizuba garin kinayi kina tankadewa kina maidawa kina sake nikawa har kigama baki daya

  4. 4

    Bayan kingama,sai ki samu busashshen shambo ki zuba ruwa sai ki barshi ya jika. Idan kinaso zaki iya jikashi kafin ki nika waken.

  5. 5

    Idan yajika,saki samu blender kisa tafarnuwa,saannan ki zuba shambo dinki da kika jika sai ki nikashi

  6. 6

    A wannan lokaci sai ki zuba ruwan dimi kadan cikin garin waken ki motsa,sai kizubashi cikin shambo dinki da kike nikawa,ki rufe blender dinki kinikashi sosai bar sai kin tabbata yayi laushi sosai

  7. 7

    Sannan ki samu kwano mai dan fadi kijuyeshi aciki,sai kisa magi fari da gishiri

  8. 8

    Sai ki motsasu da kyau,kiyita bugashi kamar minti goma kina buga kullun kosan dan yayi laushi dakyau. Sannan ki zuba yankakkar albasa aciki

  9. 9

    Sai kiaza mai acikin abun suya har yayi zafi,kiyi amfani da ludayi ko spoon kina dibawa kina zubawa cikin mai,kinayi kina motsawa har ya soyu yayi golden brown sai ki kwashe.

  10. 10

    Sai ki zuba acikin plate,zaki iya cinsa da dakakken yaji mai dadi.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
teema habeeb
teema habeeb @cook_14150092
rannar

Similar Recipes